NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH  BOOK 1  CHAPTER 2  BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Kasance da www.bankinhausanovels.com.ng  JIYA MUN TSAYA  “Ki bar Sani ya cigaba da amfana da furta Kalmar yana sona yana cika wani abu daga burinsa, ni kuma ya cigaba da tattaro cinikin markadensa yana ba ni tukwicin so, in aka hana masa wannan an tauye hakkinsa da yawa tunda ba zai iya tara kudin aurena ba, bai kamata a hana shi furta abinda yake ji game da ni a kirjinsa ba” , Cikin dariya Amina ta ce, “Ba ki da mutunci Husna” Ita ma tana dariyar ta amsa,  “Ba rashin mutunci ba ne, sauqin kai ne da iya zama da mutane. Sai dai hakan ba ya hana ni kokarin cimma burina, ba zan auri mara ‘ sana’a ba kuma ba zan auri mai Karamar sana’a ba ZAMU TASHI  ban taba tunanin yin auren soyayya ba ni auren kudi kawai zan yi’’  Adamu ya dinga yarfe gumi a saye ba tare da lurar kowa ba. Macen da yake so sunanta Husna, yau ga shi zaune kusa da ita da tazarar da bata kai takun da za’a tsaya Kirga ba, sannan tayi magana, maganar da za’a iya gane al…