MY UNCLE COMPLETE
MY UNCLE COMPLETE MY UNCLE Page 1 Tafiya suke cikin natsuwa da kamala sanye suke cikin dogon hijab Wanda yakaimusu har kasa rugume suke da alkur’ani mai girma ,niqab dinda suka sanyane yahanani ganin fuskokinsu dan wani matsakaicin gida naga sunbude mai dauki da matsaikin parking space Gidan irin gidajennanne masu komai yana acikin daki sallama sukayi alokacinda suka bude kofar falon ba laifi gaskiya falon ya hadu , sallama sukayi adaidai lokacinda wata mata take fitowa kitchen tare da ansama musu sallamar matar bazata wuce shekaru 45 ba Sannunku da dawowa yan makaranta tafada cikin murmushi Dayarce wacce tadanfi tsayi ta amsa mata tare da cire niqab din fuskarta Gaskiyafa yarinyar tahadu farace mai tsayi wacce shekarunta bazasu wuce 17 to 18 ba Tanada dogon hanci tanada manyan idanu ammafa yarinyar tayi matukar kama da matarnan Ke iman bazaki cire niqab dinne ba yau matar tafada tana murmushi make kafada tayi irinna yara shagwababbu alamun bazata cireba Tsaki dayar taja …