ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir kadai ba, ko baki son wata rana in zamo Farfesa kamar Baban A.B.U? In yi gida nawa na kaina a duk inda nake so a outside ba a A.B Bamalli Estate ba cikin kauyen Giwa? In yi family mai tsari irin na Baban A.B.U? In yi rayuwa mai tsari irin ta Baban A.B.U? Ba irin ta su Baba Barau ba Fa’izah”.  Ban san sanda na tuntsire da dariya ba. Na ce, “Ai ni na yi zaton don ka gaji da kai mu makaranta da dauko mu ne da zuwa mana visiting shi ya sa ka koma karatun don ka gaji da saya min nama, Zanirah (Bounty) Ummi (Kit-kat), ka gaji da kai mu shopping da koya mana karatu, shine ka tafi’”’.  Dariya mai suna dariya kam Yaya Aliyu ya yi ta har ya gaji, ya ce, “Fa’iza yaushe za ki daina wauta ne don Allah? Shin in tambaye ki, da can waye ya sani yi muku hidimar makaranta? Waye ya sani sai muku balangun da alawa? Waye yake sani in kula daku in ba don ina son ku ba?  Na rantse da sarkin sarakuna ba zan taba gajiyawa da hidimta miki ba muddin  rayuwata! Ko da b…