ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir gidan da maraice, ina uwar dakin Hajjah ina shirya mata kaya cikin (wardrove), ita kuma tana falo tana sallar walha na ji sallamar Baba Muntari. Hajjah ba ta amsa mishi ba, nima ban amsa ba kamar wadda akadinkewa baki. Ina jin shi yana waya da Baba Barau, Sadi, Sadisu, Na’ibi, Ibrahim yana fadin duk su hallara falon Hajjah tunda Asabar ce kowa yana gida. Na ci gaba da abin da nake yi amma daga inda nake ina iya juyo hucin Baban Kaduna da ajiyar zuciyar da yake yi akaiakai. Ba a jima ba suka shiga shigowa daya bayan daya da sallama yana amsawa a wahale. Zuwa lokacin Hajja ta idar suna ta gaggaishe ta tana amsawa. Sannan ta dubi Baba Muntari da kulawa da kauna ta manyantaka, ta ce, “Wa ya tabo Muntari ne? Wannan sammako da taron gaggawa haka?” Baban Kaduna bai tanka ba ya ciro takarda cikin breif case dinsa ya mikawa Baba Na’ibi, Baba Na’ibi ya karanta ya mikawa Ibrahim, Ibrahim ya mikawa Barau, Barau ya mikawa Sadi, Sadi ya mikawa Sani, S…