ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir kukan tare. Daga bisani da muka ga kukan ba zai amfanemu da komai ba, Zanirah ta ce, “Mu tashi mu yi sallar nafila mu rokawa Yaya Aliyu sauki”. Washe gari su Hajjah za su tafi asibiti da safe na marairaice na ce, “Hajja don Allah?” Ta ce, “Mene ne?” “Don Allah zan biku’. “Ki bimu ina?” “Asibiti wurin Yaya Aliyu”. “Ki yi me? Kai Fa’iza da rigima kike, to shige mu je”. Ba abin da na dauka illa hijabi da reportsheet dina muka tafi. Mun samu Yaya Aliyu yana shan tea da kaninshi mai binshi Mus’ab, ya hada mishi yana mika mishi bired da yankakken dafaffen kwai da (mayonnaise) yana Ci. Hajjah ta washe baki ta ce, “A’a, Aliyu lallai jiki ya yi kyau lafiya ta samu. Mus’abu an iya jinya, sai a dage da cin abinci a kan lokaci kuma yadda ya kamata yanzu ko? Tunda an ji kamshin kofar lahira’”’. Shi da Mus’ab suka yi dariya, ya sauko daga gadon da yake an cire mishi karin ruwan, ya gai da Hajjah. Abin da na fahimta duka hankalinshi kaina yake, na tsug…