ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4 Sy. Ya rufe boot din motar ya shiga Mazaunin shi zai ja motar.  Ummi ta ce, “Ya Fa’iz, Fa’iza fa ba ka ganta bane?”  Wata muguwar harara ya yi mata, ya ce, “In na ganta sai me? Sai me zan yi? Ita ba ta ganin mutane? Ba ta san ta gaishe su ba ko don UWARTA! Ta koya mata rashin tarbiyya irin tasu ta kabilu”.  Sai kawai ya ja motar ya badeni da kura. Ummi kira take “Fa’iza! Fa’iza!! Fa’iza!!!’? Amma ko sauraron ta bai yi ba.  Na durkushe a nan na soma kuka, na yi kuka har muryata ta dashe. Na daga kai na dubi dai-daikun daliban da suka rage kwata-kwata babu ‘yan Kaduna, Zaria balle garinmu. Daga ‘yan Kano sai ‘yan Jigawa, sai ko dai-daiku daga jihar Gombe da Adamawa.  Na dora hannuna aka na rafsa kuka. Duk dokina na son ganin Hajjah, Zanirah da Yaya Aliyu ya gushe, sai wani irin tukuki da zuciyata ke yi.  Wannan wace irin kiyayya ce Ya Fa’1z ke  min? Wace irin kiyayya yake yiwa mahaifiyata da ta shafe ni? Wannan ma ai rashin imani ne ba kiyayya ba. Duk irin kin da nake …