ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3 Ummi ta ce, “Wallahi ita ce”.  A dai-dai lokacin da Yaya Aliyu ya shigar da hancin motar A.B Bamalli Estate, ya yi kyakkyawan horn yaran dake kusa a kofar flat din Baba Barau suka rugo suka fidda kayan a boot suka shigar mana dasu gida.  Yaya Aliyu Boys Qtrs dinsu ya wuce bai kara kula mu ba. Su Abba na jidon kaya suna ihu wai za su ci cornflakes din ‘yan bording school. Na ce, “Wallahi duk wanda ya bude mana kaya sai na kabari ya fishi jin dad’.  Ina kwance gadon Hajja na ji shigowar su Ummi, suka shigo da kaya _ niki-niki, Ummi cike da tsegumi take ce da Hajjah, “Wai Hajja ki duba ki ga duk yawan kayan nan da muka shigo sai da Yaya Aliyu ya sake sayen kwatankwacinsu wa Fa’iza ita kadai ranta’’.  Zanirah ma ta ce, “Kuma Hajja baki gani ba, wai don dan fadan nan da Ya Fa’iz ya yi mata dazu kafin mu fita ya yi ta lallaminta tana masa wulakanci da kada ido, ita ba ta yarda ba babba”.  Hajjah ta yi kamar ba ta ji su ba ta shiga duba kaya, ta ce, “Ya ban ga kwaki ba ba…