WANNAN RAYUWAR CHAPTER 9
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 9 Shiru Hafsat tayi gaban ta na ta faman bugawa da sauri da sauri. Tunani take shin ta dauki shawarar Anty Fauziyya ta fadawa Ahmad gaskiya. Wata zuciyar tace “ki fada masa gaskiya ki huta in yana son ki a haka shikenan in ma baya son ki Allah ya kawo me son ki a haka.”+ Wata zuciyar kuma da ta riga ta kamu da son sa. Dan Ahmad ya burge ta tace mata “A’ah Hafsat kada ki fara. Ahmad ba kamar Muhammad mijin Fauziyya bane shi daman yasan ta a kuma ta fada masa amman ke fa kin tabbatar da irin son da yake miki ne da zaki fada masa salon ya zo ya gudu bayan kuma kina bakatar auren.” Dayar zuciyar yace “Ki fadi dai gaskiya ki huta Hafsat!” Kai ta girgiza. Jin tayi shiru yasa Ahmad fad’in, “lafiya kuwa? “ ‘Kago murmushi tayi tare da fad’in “Sunana…” Dakatar da ita yayi yana fadin “Ko dan ban fara miki bayanin ko ni wanene ba ko?” Kan tai magana yace “Sunana Ahmad Aminu kamar yadda na fada miki mahaifina Alhaji Aminu babban likita ne sai mahaifiyya ta Hajiya Amina. Mu shida ne a gida…