WANNAN RAYUWAR CHAPTER 7

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 7
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 7 Washe gari da safe yana tashi wayar sa ya duba ko zai ga reply din ta amman bai gani ba sai ya kawo hakan ko da jan aji ne na mata. Wanka ya shiga ya fito ya hau shiryawa. Gajeren wando ya saka da singlet yana zaune yana neman layin Hafsa. Basma ta shigo da sallama. Hannun ta rike da basket na kayan karin Yayan nata. “Ina kwana Yaya?” “Lafiya.” Ya fada yana cigaba da danna wayar sa. Kallon sa tayi dan ba haka ya saba amsa mata gaisuwa ba. Wannan yasa ta hada masa tea din sannan ta mika masa tana fadin “Ga tea din.” “Ajiye.” Ya fada yana kara trying number Hafsa da ake cewa a kashe take amman yaki yadda yana tunanin ko matsalar network ne. “Yaya wa kake nema haka ne?” Wayar ya ajiye yana kallon ta sai ya saki murmushi yana fadin “Antyn ki “ “Anty nah?” Ta tambaya. Kai ya gyada yace “Eh Amarya ta mai zuwa ba.” “Oh tana lafiya? Ko kishi take zaka angwance yau.” “Hmmm!” Kawai ya fada yana daukar tea da ta hada masa. Sha ya fara yi ya bude flask din cheaps ne da kwai kadan yaci y…