WANNAN RAYUWAR CHAPTER 5

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 5
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 5 Fauziyya na shiga gida ta fada dakin ta ta kara fashewa da wani kukan lallai ta bata rayuwar ta shin meyasa bata amshi kaddarar da ta same ta bayan afkuwar komai ta kona ga Allah ba sai ta cigaba da sabawa Allah. “Innalillah wainna illahir rajiun! Shin da ba mutu ina mai aikata zina fa? Lallai da na kasance asarar ra nazo duniya a banza na koma a babu. Na kasane yar wuta.” Ido ta runtse tana mai daga hannun ta sama tana fadin “Astagafurullah wa atubu’illaik! Ya Allah ka gafarta min ka yafe min ka yafe min dan darajar Annabi Muhammad (SAW) Allah ya yafe min ka shirya ni ka yafen min! Astagafurllah! Astagafurullah!! Astahagafurullah!!!” Abinda tai tayi kenan dan sam bata cikin haiyacin ta tsoron duniya da tsoron azabar Allah ta sa ta shiga tashin hankalin da bata taba shiga ha. Tana halin nan kanin ta Al amin ya shigo mata da kayan da ta bari a soro ko ta kansu bata bi ba. Bandaki ta shiga ta dauro alwala sannan tazo ta hau Kan sallaya tana mai kai kukan ta ga rabbi…