WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10 “Ummu ki fito me kike yi ne? Ko so kike mu rasa flight ne?” Anty Zainab ta fada. Ummu dake daki tace “Anty gani nan!” Ta fito sanye da dogowar riga yar saudi maroon kala. Wacce ta amshe ta ta kara fito da hasken fatar ta. Yadda Ummu tayi kyau fatar ta ta kara haske da taushe saboda gyara da ta samu. Nikaf ta fara kokarin sakawa Anty Zainab tace “Wato shi kika tsaya nema zaki makarar da mu ko?” “Sorry Anty!” “To ba zaki saka ba. Ai kinsan facemask zasu ce ki saka dan ki sa su tsaida mu suna magana ko? Maza ki cire malama!” Fuska ta bata tace “Kai Anty dan ai ta kallo na?” “Menene dan an kalle ki to?” “Haram dai gashi kin sa na kara kyau!” Ta kara magana tana turo baki! “Au haka kika ce ko?” Tayi kwafa tayi gaba. Ummu ta bita a baya tana turo baki. A compound suka samu su Yaya Suleiman a mota. Kan Ummu ta karaso Anty Zainab har ta shige mota. Yaya Suleiman dake zaune kusa da driver ya juyo yana fadin “Ya kuka dade?” “Ga yarinyar da ta zaunar damu nan!” Ummu ya kalla yaga yadda tak…