TANA TARE DANI CHAPTER A

TANA TARE DANI CHAPTER A
TANA TARE DANI CHAPTER A ANAS      K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.             Da yammacin ranan Asabar misalin k’arfe biyar da mintuna aka. Ruwan sama akeyi me ni’iman gaske, ga wani iskan dake hurawa me kad’a bishiyoyi da flawoyi, ko ina ya d’au sanyi. Tsit kukeji a garin, yara da manya, maza da mata kowa na cikin gdajensu, masu tafiya akan hanya kuwa sun faka gu d’aya, motoci dabasu fi a k’irga ba ke wucewa time-to-time. Can k’ark’ashin wata bishiyar ’yim na hango wasu samaruka guda hud’u wanda barasu gaza kuma barasu fi shekaru 17-18 ba.         Daga nesa nake, amman hakan be hana ni tantance kyakkyawan cikin wad’annan samarukan ba. Wani kyansan ma sanda na gama k’arisowa, fari ne yellow shar da gashi kwance a duk sassan jikin d’an Adam da akasan na tsirar da gashi. Gashin kansa nada yawa saidai bawai afro tayi ba saboda tsantsin gashin bai tsayuwa, luf-luf yake kwance a kansa, bak’i k’irin yana yalk’i wane yasha mai.       Saje ne kwance akan farar fatar fuskarsa wanda da a…