NI DA AMARYATA COMPLETE

NI DA AMARYATA COMPLETE
NI DA AMARYATA COMPLETE BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM Da sunan ALLAH mai rahma mai jink’ai, ya ALLAH kabani ikon fad’in abinda zai amfani Al’ummarka, ka tsarkake harshena daga fad’ar abinda zai cutar da Al’ummarka. Amin ya “RABBI”. Assalamu alaikum, ina mai farin cikin sake had’uwa daku asabon littafina, akaro na 4, ina godiya ga d’umbin masoyana aduk inda suke, “UBANGIJI ALLAH” yabar k’auna. Nagode?? Zanyi amfani da wannan dama, domin taya d’umbin Al’ummar MUSILMI shiga sabuwar shekarar musulinci, ALLAH ya albarkacemu da rahamarsa.     ?HAPPY NEW YEAR? ……….’Yammata biyune ke tafiya, cikin nutsuwa, jikinsu sanye da kayan makaranta, (uniform) pink d’in wando da farar riga, sai farin hijjab daya tsaya musu iya k’ugu, dan baikai d’uwawunsuba, bayansu goye da jakar makarantarsu (school bag).        “Sukaja birki abakin titin da d’umbin  d’alibai ke tsaiy tsaye suna jiran motar makaranta,wash ALLAH!!!, d’aya daga cikin ‘yammatan ta fad’a.  D’ayar ta bita da kallon mamaki, kai fareeda badai gajiyaba??…