MATAR MUTUM COMPLETE
MATAR MUTUM COMPLETE _WRITTEN BY_ *FATIMA ISAH* ( _MRS. OMAR_) _PAGE 1_ A hankali take tafiya d’auke da tiren talla a kanta cikin sanyin jiki da alama tunani take. Yanayinta kadai zai sa kagane nutsatsiyar yarinya ce bakin titi take tafiya wasu samari na zaune a bakin wani shagon kaya, d’aya daga cikinsu ne yace. “Kai jama’a kudubi wata yarinya a chan tana tafiya,she is beautiful” Dukkansu suka dubeta banda mutum d’aya.. wanda yayi maganar, shi ya sake magana “Kai! kunsan matsalar yarinyar nan kuwa?” Dukkansu suka amsa da a’a, banda dai mutum d’ayan saurayin nan. “Matsalarta d’aya,she is sojan tire” dukansu sukasa dariya a hankali naga ya dubi saurayin nan da baya magana yace masa “Look my friend kowa na magana kayi shiru wannan wacce irin rayuwa ce?” Sai yanzu ya d’ago kanshi. Ya salam wani kyakkyawan saurayi ne nagani wanda bazai wuce shekara 30 bah, cikin isa ya fara magana ya furta “So what ina ruwana da ita” Mai surutun nan ya kuma fad’ar “Haba HAMEED…