ZABIN SAMHA CHAPTER 8 ZABIN SAMHA CHAPTER 8 Bangaren su Samha kuwa, tsaye take da Jabbar a cikin restroom hanunsa rike da camera din yana cigaba da mata video. Wani irin dariya ya sake yana fadin “Samha, Samha kenan, wato ina ajiye miki sakon kin zata shine, kika zo jikinki na bari? Ya tambayeta yana wani irin dariya. Samha ta hada rai sai faman zabga mishi harara takeyi “Haba ki dan saki fuskarki mana, kinsan kinfi kyau idan kina fara’a”. Ya karasa maganar yana cigaba da mata dariya. Samha ta dago paper dake hanunta ta soma tambayarshi “Daman kaine ka rubuta wanan sakon ka ajiye mun?” “Correct!” Ya bata ansa yana cigaba da murmushi. “Ai inata tunanin yanda zanyi na janyo hankalinki zuwa gareni. Shine nace bari nayi amfani da sunan Sabah. Sai gashi nan kinyi tsuntsu kinzo”. Ya fada yana dariya. “Dakata mallam! Wanan wani irin shashanci da rainin hankali ne? Eh!” Samha ta fada mishi a tsawace. Nan kuma hankalinta ya dawo kan camera dake hanunsa yana mata video. Cikin sauri ta kawar da fuskanta gefe tana fadin “me ku…