ZABIN SAMHA CHAPTER 7 ZABIN SAMHA CHAPTER 7 Wuri suka samu suka zauna suka yi shiru barin ma khadija da jikinta yayi bala’in sanyi ganin tsohon saurayinta Alamin. Hawaye masu zafi ne suka soma gangaro mata ta sa hanu ta soma gogewa. Amjad yayi shiru yana kallonta. Cikin sheshekar kuka ta soma fadin ” ban san me nayi dana cancanci haka ba, wai kawata da saurayina suci amanata, musamman Alamin wanda nabashi zuciyata halak malak, meyasa zasu ci amanata haka? Me na musu?. Da acan baya nace bazan kara soyayya ba amma everything changed when i met you Amjad” ta karasa maganar tana rushewa da kuka. Amjad shiru yayi yana dubanta tana kukanta daga bisani ta cigaba da fadin ” nasa rai a wanan fitan namu, komai zai tafi yanda ya kamata, nida kai zamu samu mu fuskanci juna sosai, amma gashi wancan yazo ya bata komai.” Amjad ya cigaba da dubanta daga bisani ya kira sunanta a hankali ” khadija….” Khady ta dago kai tana dubansa da jajayen idanunta still bata daina kukan ba. Amjad yace “ki daina kuka khadija, inaso ki share haw…