ZABIN SAMHA CHAPTER 3
ZABIN SAMHA CHAPTER 3 Samha ta zaro ido tana girgiza mata kanta alamun karta mata haka. Kwalla ya ciko mata idanunta. Murmushin mugunta Aliyah ta cigaba dayi. Ta kamo karshen gashin samha zata hada da lighter din kenan kamar daga sama sukaji an watso musu ruwa. A firgice suka juyo sukaga wani mutum rike da bokiti da mop a hanunsa. Da alamun daya daga cikin masu sharan makaranta ne.+ “Meye kuke haka?” Ya tambayesu yana kallonsu daya bayan daya. Shiru sukayi basu ce komai. Aliyah sai faman galla masa harara takeyi. Kare musu kallo yayi sa’anan yace . “Badai cin zali kukeyi ba. Me ta muku da zaku kamata ku daure haka?” Ya tambayesu. Ya juyo ya dubi Aliyah sa’anan yace ” keh kuma kyakyawar yarinya kamar ki amma zuciyar ki babu kyau? Konata zakiyi?” Daya daga cikin yan matan ne tace ” kai tsoho ina ruwanka. Bamu san surutu, ka wuce ka bamu wuri kaje ka cigaba da aikin sharanka. Ta fada mishi cike da fitsara. “Ni kike ce ma tsoho, toh bari inje in kira daya daga cikin malaman naku suzo su ga abund…