ZABIN SAMHA CHAPTER 2
ZABIN SAMHA CHAPTER 2 Washe gari da safe samha ta tashi, Yau kam batada lectures sai zuwa karfe biyu na rana. Bayan ta shiga bayi ta wanke bakinta ta fito taje dakin anty fanneh don ta gaisheta, ta sameta tana faman shirin zuwa aiki. “Ammi ina kwana” ta gaishe ta. “Lafiya lau baby, kin kwana lafiya? ya ciwon kan yanzu. Hope dai ya lafa miki?” Anty fanneh ta tambayi diyarta. Samha ta bata ansa da eh ya lafa mata.+ “Toh nasan yau bakida lecturers da wuri, zan baki dan kudi keda lami zuwa anjima kuje kasuwar kingsway ku danyi mun cefene. Kinsan munada bako yau zai zo, so inason a dan dafa mishi delicacies.” “Kai ammi wai dan Allah dan yaron mutumin nan zai zo zaki wani ba kanki wahala kiyi girki? Sai kace wani babban bako zamuyi. Ai ko snacks da ruwa aka bashi idan yazo sun isheshi.” ” Kuji mun yarinyar, dan nashi kike ce ma yaro? Toh ashekaru dai ya girme ki nesa ba kusa ba don har shekara hudu ya baki da zaki ce mishi wani yaro. Kinga idan Allah ya yarda ma very soon shima zai zama dana. Kin…