ZABIN SAMHA CHAPTER 15 KARSHE
ZABIN SAMHA CHAPTER 15 KARSHE Samha muryanta na rawa tace ” nan fa kitchen ne ya kakeso tayi? Knocking zatayi kafun ta shigo ko meye? “. Tsaki Sabah ya buga cike da jin haushi ya juya ya fice daga cikin kitchen din. Ajiyar zuciya Samha ta sake nan take ta nema yunwar ta rasa ta ajiye the plate din abincin a gefe ta fito. Ko data fito bata ga kowa a parlourn ba ta soma kwadawa sophie kira, taji shiru ba’a ansa ba. Haurawa sama tayi tunani kala kala na mata yawo aka don tasan yarinyar ba fada zatayi ba. Amma toh da Ammi ce tazo ta tadda su a hakan fa? Ya zasuyi? Nan take ta tsinci kanta cike da tsananin fargaba. Da dare misalin karfe bakwai da rabi suna zaune kan dining suna cin abincin dare gabada’yansu sun halara. Anty Fanneh da Abbah suketa faman hiransu banda Sabah da Samha da sukayi shiru suna sauransu. Sabah sai faman latse latsen waya yake Samha tanata satan kallonsa ta kasan idanunta. Suna cikin haka taji wayarta tayi vibrating kusa da ita allamun sako ya shigo. Daukowa tayi ta som…