ZABIN SAMHA CHAPTER 14

ZABIN SAMHA CHAPTER 14
ZABIN SAMHA CHAPTER 14 “Abba har ka dawo?” “Na dawo” Abba ya fada yana kare musu kallo daya bayan daya wanda yasa suka ja jinin jikinsu. Barin ba Samha wace tafi tsorata kirjinta sai buguwa yake da karfin gaske. “Ya naganku anan haka?” Sabah ne yayi saurin bashi ansa da “Wlh Abba, gajiya ce. Bansan lokacin da baccin ya tafi damu haka ba” Shiru Abba yayi bai sake cewa komai ba, yana aiyano abubuwa da dama aransa. Kardai shakuwar dake tsakanin yaran nan ya soma wuce gona da iri. Wata zuciyar ce ta fada mishi “kilan da gaske ne gajiyar ce kawai tasa bacci ya kwashe su a hakan. There’s nothing to be worried about” duk da hakan bai gamsu ba ya dubesu yace “kun ci abinci kuwa?” “Eh munci Abba”. “Okay good. Ni zan haura sama na watsa ruwa tukana na koma asibiti” Yana gama fadin haka ya juya ya haura sama zuciyarsa fal da damuwa tunani kala kala na masa yawo aka. Abba na tafiya, Sabah da Samha suka juyo suna kallon junansu. Ganin damuwa rubuce fal a fuskar Samha yasa Sabah ya girgiza mata kansa allam…