ZABIN SAMHA CHAPTER 13
ZABIN SAMHA CHAPTER 13 Yau kwana biyu kenan da tafiyar Madina. Amjad, Zack, Aliyah da khadie zaune suke a cikin class suna tataunawa. Zack yace “tab daman Teacher Sameer da Samha sunyin sharing irin wanan past din? Amma Amjad, kace Khaleesat din tanada kyau sosai?” Ya karasa maganar yana murmushi yana shafa sajensa. Harara Aliyah ta watsa mishi tace “meye haka kuma?” Hakuri ya soma bata yana sosa kai. Tsaki ta buga mishi sa’anan ta dawo da dubanta ga khadie tace “khadija ya kike tunanin za’ayi kenan?” Zack yace “ya kamata mu taya khaleesat kwato soyayyarta daga wurin teacher sameer, ko ya kuka ce?” Dukkansu suka gyada kai suka yarda da wanan shawaran. Sameer kuwa yana cikin office dinsa sai faman trying number khaleesat yakeyi amma sai yaji a kashe. Gabadaya hankalinsa a tashe yake ya gagara samun sukuni. Yana zaune yaji anyi masa knocking a kofa, dagowa yayi yana duban kofar sa’anan ya bada izinin shigowa. Su Zack ne yaga sun shigo suka soma gaishe shi, ya nuna musu wurin zama.+ “Ya lafiya?” Y…