ZABIN SAMHA CHAPTER 12
ZABIN SAMHA CHAPTER 12 A daren ranar dai Sameer yana ajiye Madina a gida, khaleesat ta kirashi a waya tace tana son ganinsa. Gidansu ya karasa yana zuwa kofar gida yayi parking ya kirata a waya yace ta fito. Tana fitowa ta karaso cikin motar suka gaisa. Khaleesat ta kura masa ido na da’an lokaci tana kallonsa taga gabadaya duk yabi yayi wani iri, kuma tasan ba komai bane yake damunsa illa son Samha da yake dawainiya da, cikin zuciyarsa. Murmushin yake ta da’an sake sa’anan tace “yau ka fita da yar’ budurwan taka kenan kun zaga gari, toh ya? Ka samu ka fallasa mata sirin zuciyar naka kuwa?”. Sameer yayi shiru yana jinta daga bisani ya gyada kai yace “eh kusan haka”. Gaban khaleesat ne ya fadi, amma tayi kokari ta dannetace “toh daka gaya mata me tace?” “Ban sani ba wlh”. “Baka sani ba kuma?” “ina cikin fada mata aka samu wani da’an accident so babu samu mun karasa maganar da mukeyi ba”. Khaleesat ta da’an nesa sa’anan tace “hmm toh shikenan naji, amma kafun ka samu ansar naka daga gareta, ni ba…