ZABIN SAMHA CHAPTER 11
ZABIN SAMHA CHAPTER 11 Shiru Madina tayi daga bisani ta cigaba da fadin ” i was wrong, bai kamata na fadawa Sabah wanan maganar na cewa muyi pretending muna soyayya saboda kar iyayyen mu su gane ba.” Shiru Samha tayi tana sauraronta don itama jikinta ne yayi mugun sanyi data tuno cewa suma they are hiding their relationship from their parents . “Big sis…Anty na..” Madina ta soma kiran Samha, amma ina Samha ta rigada tayi zurfi cikin tunani. Sai da Madina ta dan tabota tukuna tayi firgiti ta dawo hayacinta. Madina ta dubeta tace “Big sis lafiya kuwa? Inata magana naji kinyi shiru” Murmushin yake samha ta sake sa’anan tace “lafiya wlh. I’m okay. I just zoned out ne kawai”. Madina tace “okay, daman inaso na fada miki cewa inaso dani dake da Sabah mu zama good friends, da fatan dai babu matsala zaku karbe ni hannu bibiyu?” Gaban Samha ne ya fadi dataji Madina tace tanason ta kulla abota da Sabah, kar dai kirkinta yanaso yajaza mata? Murmushin karfin hali ta sake kirkirowa ta sakar mata sa’anan …