ZABIN SAMHA CHAPTER 11

ZABIN SAMHA CHAPTER 11
ZABIN SAMHA CHAPTER 11 Bangaren Sameer kuwa, bayan sun koma school kowa ya watse ya kama gabansa. Sameer ya biya wajen wata friend dinsa mai suna Khaleesat. Khaleesat ta kasance tanada babban wuri na cin abincin kusa da makarantar su. Sun jima suna abota tare kuma ta jima tana mutuwan son Sameer shine dai bai bata fuska akan suyi wata soyayya ba. Khaleesat tasa aka kawo masu lemu masu sanyi sa’anan ta nema wuri ta zauna kusa dashi tana tambayarsa ya trip din nasu. Sameer yace mata lafiya lau. Khaleesat ta da’an nesa tana dubansa sa’anan tace “ya ka samu kaga yarinyar malamin naka kuwa?” Sameer ya gyada mata kansa yace “eh” Tace “toh how was the reunion?” Sameer yayi shiru yana dubanta yace “meyasa kikeso ki sani?” Khaleesat tace “haka nan. Kawai i just want to know. Baccin haka baka ce nan da yan kwanaki bane birthday dinta ba? Ai nasan saboda hakan ka dawo don ka taba fadamun cewa a da tun tana karama baka taba missing birthday dinta”. Sameer yace “Khaleesat kenan, you think too much”. Khaleesat…