ZABIN SAMHA CHAPTER 1
ZABIN SAMHA CHAPTER 1 Samha Abdullahi Bamanga, zaune take cikin aji a seat din dake row na biyu da littatafai zube a gabanta. Sanye take cikin kananan kaya. Bakar riga da pink skirt ne a jikinta kuma kayan sun amshe karamin jikin ta, sai dan karamin bakin dankwalin data daura a kanta. Gyara zaman glasses din dake manne bisa fuskarta tayi, tana cizon murfin biro dinta a hankali kamar yanda ya zame mata jiki. Gabadaya tunaninta baya kan abunda ake koyarwa. Hankalinta da tunaninta sun karkata zuwa ga Amjad Tafida dake zaune a seat din gaba. kurawa gefen fuskar sa ido tayi, koh kyaftawa batayi, fuskarsa take tabi da kallo tana jin kamar ta janyo shi kusa da ita tasa hannu ta shafo kyakyawar fuskarsa ko zata samu sassauci a zuciyarta. Gangar jikinta ne yake ajin amma ruhinta gaba daya ta tafi da tunanin amjad. Tana wata uwa duniyar tunaninshi.+ Ba karamin crushing samha takeyi akan Amjad ba don tun suna aji daya ta kamu da sonshi. Amjad kyakyawa ne sosai kuma na ajin farko, kasancewarsa Haus…