YANKAR KAUNA CHAPTER B
YANKAR KAUNA CHAPTER B Tashi tayi ta ajiye kundin sirrin a cikin wardrobe. Bata tsaya ko ina ba se sashin rufaida, tana zuwa ta rungume ta, addua take mata godiya, fadi take + “kin tseratar da d’a na daga hallaka, Allah ne kadai ze biyaki”. Kuka sukai sosai sannan su ka yi shiru, hakan ya sake tayar da shauk’in son umair a zuciyarta. Barcin da batayi ba kenan ta kwanta cikin yaranta, tana addua har sulusin dare sannan ta tashi ta yi salloli da addua. ??? Akwana a tashi shekaran Umair biyu da Rasuwa, rabon Rufaida da farinciki tun rasuwan Umair, Alh Zunnurain ya kafa mata maaikatan Zane zane , dukiyanta kuma massallatai da rijiyoyi ta gina duk d sunan Allah ya kai Rahma zuwa ga mijinta. Zaune take ta na Zane, ba abinda ya fado mata a rai se sanda take da cikin khadija. Ranar hana ta Zane yayi, duk motsin da tayi yana manne da ita, alkaura da kalaman soyayya da dadadan kalamai Kuka tasaki sosai, ji takeyi kamar lokacin ne taji sak’on rasuwar Umair. “Rufaida me ke faruwa ne, yanzu takwara na…