YANKAR KAUNA CHAPTER A

YANKAR KAUNA CHAPTER A
YANKAR KAUNA CHAPTER A Shimfida+ Gwandu babban gari ne a jihar kebbi, masarauta ce guda mai ri’ke da sandar mulki, gari ne da ya Tara manyan ‘yan boko da ‘yan kasuwa. Gari ne da ya mallaki babban kwallejin ‘yan mata na tarayyah wato (FGGC GWANDU) wanda akan sami dalibai daga kowani sassa na kasar nan da Nijar da ke makwabtaka damu. Gwandu gari ne da yake fama da kwararowan Hamada (desert encrochment) a dalilin haka lokacin sanyi akan samu sanyi mai tsanani a garin haka zalika lokacin zafi yakan yawaita da har mutan garin kan kwana a waje.9 Hausawa suka rinjaye garin amma akan sami tsirarrun fulani a ciki. Akwai wani abu guda da mutanen gwandu ke dashi wato KARAMCI, suna da dadin zama duk inda ka same su. Sukan maida dan kowa nasu ba tare da nuna bambamci ba.1 Tsayawa fadin karamcin mutanen jihar kebbi ma bata lokaci ne, gari ne mai cike da albarkan zumunci da son juna,1 ???10 {1} “Keeeeeeeeeet!!” mota k’irar marsandi ce ta bada wannan k’arar a dalilin birki da motar ta taka ba cikin shiri ba,…