YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE

YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE
YANCIN MATA CHAPTER B KARSHE * Da kallo Ummee ta bishi tana tausaya masa. + Hafiz kuwa yana fita yayi murmushi yace “Wasa farin Girki.” Alwala yayi ya huce masallaci. Har suka dawo Hafiza bata farka ba , cikin sanyin jiki yayi musu sallama ya tafi gida. Abbie ne ya kalli Ummee yace “ya kike ganin zamu b’ullowa Wannan lamarin?”. Ajiyar zuciya tayi tace ” ni abun ya fara bani tsoro wallahi kalli yadda Hafiza ta koma lokaci d’aya anya kuwa ba asiri akayi mata ba?”. Abbie yace “Allah ne masani mu bari ta farka muga yanayin jikin nata, ni mijin tane yake bani tausayi ji yarda ya koma shima kai Hafiza tayi dacen miji mai sonta.” Ummee tace “nima addu’ar Dana kewa Hanifa kenan Allah ya bata miji kamar Hafiz.” Har dare yayi amma Hafiza bata farka ba . Hafiz kuwa yana can gida amma ya kasa komai gani yake gidan yayi masa girma , jinsa yake kamar wani sabon maraya . A lokacin ya kuma tabbatar da irin son da yake yiwa Hafiza , a fili yace “kiyi Hak’uri Hafiza banyi niyar fad’a miki yanzu ba amma ganin yadd…