YANCIN MATA CHAPTER A

YANCIN MATA CHAPTER A
YANCIN MATA CHAPTER A * Tafiya take tana cikin sauri tana duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hannun ta , yarinya ce y’ar kimanin shekara goma sha biyar tana sanye da dogon hijjabi da alama daga islamiyya ta dawo , titin tas babu kowa gashi magariba ta gabato hakan yasa take ta sauri dan tasan halin unguwar tasu yanzu sai a sace mutum . + Wata mota ce bak’a k’ira Benz tazo ta gifta yarinyar a guje , cike da tsoro yarinyar ta cigaba da sauri kamar zata tashi sama , cak motar ta tsaya tare dayin reverse har ta dawo inda yarinyar take Wasu maza ne suka fito daga motar basu tsaya wani tunani ba suka fesawa yarinyar wata hoda a fuska , nan dake tayi baya zata fad’i suka taro ta suka saka ta a mota suka cigaba da gudu. Sabon sirinji suka d’auko suku dibi jinin yarinyar sannan suka rife sirinjin , basu tsaya a ko ina ba sai a bakin wani asibiti d’aya daga cikin mazan ya d’auki wannan jinin ya shiga cikin asibitin . Direct lab ya nufa yana zuwa ya mik’a musu kamar yadda suka saba , gwajin cutar k…