WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE

WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE
WAYA SAN GOBE? CHAPTER B KARSHE Fadila tayi murmushi sannan ta tada mota iftihal tace “anty Abba yace munyi kyau wai na zama ‘yar gatan anty ni ‘yar gatanki ce wai anty?”ta shafa kanta da daya hannun nata tana murmushi tace”iftihal ke ‘yar gata na ce mana” Minti arba’in suka qarasa gidan da yake safiya ce babu yawaitar mutane sai ‘yan uwa na jiki sosai,su hajja gana(kakarsu ta gun uba) umma a’i anty hafiza rumaisa da sauran ‘yan uwa na nesa da na kusa,Fadila ta fada jikin hajja gana tana cewa bari na more cinyar ‘yar tsohuwa” hajja gana ta sa dariya da yake sunfi shiri da Fadila fiye da farida”more abinki kafin kema Allah ya kawo miki masu more taki”murmushi fadilan tayi sannan suka soma gaisawa da yan uwan hajjar na tambayarta mai gidan tace lpy lau yana ma gaisheki Kafin azahar gidan ya tumbatsa da jama’a,ko ta ina,bayan azahar kuma da kadan sai ga family din aliyyu momi ce kawai banda ita,cikin bedroom din farida sukayi zamansu anata karbar baqi Rabi’ah ta kalli fadila lokacin da take…