WANNAN RAYUWAR CHAPTER 2
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 2 A haka rayuwa ta cigaba da tafiya sakanni na komawa minti na, minti na komawa awa, awanni na komawa kwana, kwanaki na komawa satitika, satittuka na komawa wattanni. Dan har anci wata uku da auren kamar yau akai abin ake gani.+ Muhammad ya samu aikin koyar wa anan wata primary but gwamnati ce ta dauke shi yana daukar albashin sa dubu talatin da wani abu. Watan sa hudu da fara aiki ya samu admission inda zai juya degree din sa anan BUK sai dai ma’aikatar su tace sam ba zata bashi inservice ba saboda bai jima da fara mata aiki ba. Da ya zauna yai tunani sai yaga komai na Allah ne tinda ya samu admission din nan gwara yai fara karatun aiki ai daman bai zama lallai yayi ba ko kasuwancin sa Allah ya bawa sa’a sai ya zama wani abun. wannan yasa ya hakura da aikin kan cewar in ya gama karatun zai koma. Tin kan ya ajiye da yai shawara da Hajiyar sa itama cewa tayi yaje ya karo karatun bai san gaba mai zai zama ba. Wannan yasa ya ajiye da gayya dan shawarar Hajiyarsa. A w…