WA NAKE AURE CHAPTER A

WA NAKE AURE CHAPTER A
WA NAKE AURE CHAPTER A Tsugunne take idonta sai ruwa yake, saboda Hayak’in dake shigar Mata Ido,dakyal tasamu wutai ta kama, mik’ewa tayi tare da dafe kanta dake mata wani irin ciwo,komawa tayi bisa k’ujera yar tsugunni, ta cigaba da tsintar shinkafar ta Yar hausa dake cike da tsakuwa cikinta, tafi awa biyu tana tsintar shinkafar, ta kusa idawa ne taji shigowar sa,yadda ya saba babu sallama gaban ta ya fad’i Amma ba ta nuna hakan ba, ji tayi an kife tsakuwar cikin shinkafar datake gyarawa cikin sauri ta d’ago idonta ta kalleshi.+ Ko a jikinshi,saima wani kallon banza da yakeyi mata,kanta kawai ta daga tare da cewa”haba Hayatu wane irin abu ne hka?ina aiki ka maida Mani aiki baya?” Zama yayi Bakin barandai data gewaye tsakar gidan,”tun sha biyu akawo maki cefane amma har yanzu baki gama girkiba,k’arfe biyu da rabi yanzu” “Amma ai tun lokacin da ka shigo da icce nace baka d’anyu ne,basu cin wuta” Dogon tsaki yaja tare da cewa”lallai yarinya,ai ko nine mijinki baki isa,insawo abu kice in ma…