TAURA BIYU CHAPTER A
TAURA BIYU CHAPTER A *_MAMUH GEEE_* _*TAURA BIYU….*_? _Mi amor-mi vida_…. _viawattpad@mamuhgee_ 2 *1* _Bismillahir-rahmanirraheem_. *B* abban gidane sosai daya qunshi 6angarora acikinsa sbd yawa da zuriar gidan sukeda shi,, Gidane tsohon gini irin na masu arzikin lokacin baya daya gabata, Mal Zubair shine mamallakin gidan da ahalin gidan gabaki ‘daya, Ya rasu shida Mai ‘dakinsa Fatima sunbar ‘yaya hudu duka maza,,+ Baba malam hayatu shine babba agidan yanada tsananin zafi da fa’da, Sam baya kar6ar uzuri ko kuskure duk da kasancewarsu malamai masana addini,2 Baba malam shine Mai zartarda duk wani hukunci acikin gidan Kuma ya zartu Koda baiyiwa kowa dadiba. yanada mata biyu inna hindatu da iya lami, Inna hindatu bata ta6a haihuwaba iya lami ce keda ‘yaya bakwai, _zayyanu, auwalu, dahiru,Musa,mustapha, abudullahi da sani_. Baba shehu shine mabiyin baba malam Kuma shima kusan duk halinsu ‘daya da baba malam illai shi Yana da’dewa baiyi fadan ba, Matarsa ‘daya shi,mama salamatu Sai ‘yaya …