SAUDALA CHAPTER A

SAUDALA CHAPTER A
SAUDALA CHAPTER A Wata dariya ce ta kusa kufcewa saudala , amma sai ta danne ta cigaba da cewa ” karki sake ki fito tsakar gida yanzu, ki bari sai da safe in ba haka ba anan zaki kame har sai wani daren , Iya da take kwance cikin kashi kai kawai ta daga jikin ta na rawa, Tace “in kika fadawa wani wannan abinda ya faru shikenan sunan ki gawa , Cikin rawar baki iya tace ” kwarankwasi bazan fada ba , Saudala cikin tsawa tace ” rife idon ki Tsawar  da tayi yasa iya kuma sakin wani kashin? , cikin sauri ta rife idon , Mikewa saudala tayi ta wata tafiya kamar aljanar gaske tana bude hannu kamar tattabara , Tana zuwa daki ta dinga dariya kamar mahaukaciya , Tace ” zaki gane kuran ki iya , badai ni kika zaga ba , In sane nace karta fito sai da safe yadda zan kuma cin dariya ?? Tashi tayi ta wanke fuskar ta ta cire kayan jikin ta ta kwanta, Tunda saudala ta fita iya take kuka tana fadin ” shikenan karshe na yazo  aljanu sun fara bibiyata , kai dole gobe nabar gidan nan dan bazan iya zama wannan aljanar ta k…