RAYUWAR ASMAU CHAPTER 15 KARSHE
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 15 KARSHE Da dare da wuri ta mishi girki kafin ya dawo, ta shige d’aki tana gama sallolinta tayi shirin kwanciya, doguwar riga ta saka iyakar gwiwa pink, mai santsi dabin jiki, tayi kyau sosai, mukulli ta saka ta rufe d’akinta ta haye gado tayi addu’a ta kwanta. Aslam kuwa tinda ya fita da yamma yaje gidan Momy. Tambayar da Asma’u tayi ya amsa da tana lafiya. Daga nan Asibiti ya biya, sai da akai magariba ya taho gida. Yana driving ne amma zuciyar sa na can tunanin halin da Asma’u take ciki. Bai son damuwar ta bai son bacin ranta. Dole ya san yadda zai dawo mata da farin cikin ta. Sanda ya isa gidan kamar yanda ya zata, tayi barci ko motsinta bai jiyo ba, d’akinshi ya shiga ya watsa ruwa yayi shirin kwanciya sannan ya fito ya zauna yaci abincin data girka mishi, hankalinshi duk naa wurinta harya gama. A hankali ya murd’a Kofar d’akinta, jinta yayi a rufe, kamar yadda ya zata. komawa dakinshi yayi ya dauko makullanshi yazo ya bude a hankali ya tura kofar ya shiga. K’ara…