RAYUWAR ASMAU CHAPTER 14

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 14
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 14  lokaci kadan ta fita a haiyacin ta. Momy da Zainab suna waje ciki kuma likitoci ne akan ta. Aslam kuwa yana gefe ya rasa abinda yake masa dadi. Sam sam baya son ganin ta a irin wannan halin bama da ya dauko ta zazzabin da ke jikin ta yai zafi sosai. Ruwa suka juna mata bayan sun mata allurai. Bacci ne ya dauke ta amman da ka kalle ta zaka san ba baccin dadi bane. Duk ta rame ta dada haske. Idon ta ya zurma. Sosai Momy ke tausayawa Asma’u ita bata so ma canjin nan da akai ba. Taso su bar ta wajen Sabir din ta samu sabon farin ciki. Tabbas in har Asma’u bata son Aslam a yanzu ita ta dauki alkawarin sashi ya sake ta. Aslam ma ya kasa zaune bare tsaye yana gefen gadon ta. Da ka ce ya tafi gida ma cewa yayi shi zai kwana da ita. Haka aka barshi a gun ta. Ranar bai kwanta ba kallon Asma’u ya tsaya yi sai kace sabuwar hallitta. Yana son Asma’u yana kaunar ta yasan da bai same ta ba da yayi babbar asara. Ba abinda zai ce da Sabir sai godiya dan yai masa abu da bazai taba mantawa …