RAYUWAR ASMAU CHAPTER 13
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 13 Haka canji ya dinga samuwa wajen Aslam. Dan har fita yake hana Munasha.+ Sosai ta shiga hankalin ta. Dan taga ya dawo Aslam din shi na farko. Wanda kwarjinin sa ya dadu, shi wani lokacin Mamakin mai ya hada shi da Pretty yake yi Haka zai je gun Mami yai ta cewa, “Mami number Asma’u nake nema.” Sai dai Mami ta dauke kai in ya ishe ta. Ta ce, “Me zakai mata?” “Mami ina son jin muryar ta ne, ina son sanin halin da take ciki.” Dariya Mami take in ya fadi haka. Tace, “Aslam sai yanzu kake son sanin halin da take ciki, a kalla shekara biyu rabon ku baka taba tunanin haka ba sai yanzu.” Yana mamaki in Mami ta ce, sun shekara biyu basa tare dan shi gani yake kwana ki ne. Ganin yadda Aslam ya daina sakar mata dan ba inda take zuwa ma. Kuma duk masu aikin nan ya rage su. Gashi ya amshi kudin sa dake gun ta. Wannan ya tada mata da hankali har ta dau aniyar koma wajen Bokan ta. Shirye shirye tafiya ta fara ba tare da tasanar da shi ba. Haka ta dauki hanyar nijar. Agidan kawar ta ta sau…