RAYUWAR ASMAU CHAPTER 12
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 12 Da dare akai dinner inda yan mata sukai ankon wani pink material. Amarya kuma ta saka golding kala, ango ma golding shadda ya saka. Asama’u kuma ta saka Dark blue din material sosai tayi kyau.+ Sir Sabir ma Blue shadda ya saka sai ya fito shima kamar angon Asma’u. Anci ansha an yi liki, duk wanda yaga Asma’u sai ta burge shi dan komai nata da banne ga kyau ga jikin yana dauka. Samarin wajen sun yaba da ita. Sir Sabir kuwa sai kareta yake. Sai da sukaje suna liki ne, kuma sai kuka taga ga Mami ga Yaa Buhari gata ammn ba Dady. Sosai ta sa mutane da yawa kuka a wajen. Anyi taro lafiya an tashi lafiya. Inda washe gari aka dau amarya aka kai ta gidan mijin ta dake rijiyar zaki. Gida ne katon gaske dan Dady ne ya gina masa shi. haka nan an zubawa Zainab kaya sosai. Sai da angwaye suka je sanna suka taho Asma’u na zolayar Zainab Gida su Asma’u suka tafi da su Maimuna da Maryam. Aka bar amarya da ango su kadai a gida. A gida ma wasu dayawa duk sun tafi dan daga Momy sai matar Uncle …