RAYUWAR ASMAU CHAPTER 11

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 11
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 11 Zama yayi shima yai murmushin kawai. Mami ce ta sauko. Hira suka dan taba sannan yai masu sallama ya tafi. Zuciyar fal da tunanin Asma’u. Yana kaunar Asma’u son Asma’u yai masa wani irin kamu. Asma’u kuwa tana shiga daki ta fada kan gado. Ido ta lumshe ba wanda ya fado mata sai Yaa Aslam, Ta jima tana juyi duk ranta ba dadi sannan ta mike ta shiga cire kaya. Tana gamawa ta fada bandaki wanka ta fara. Tana gama wa ta tayi alwala. Sai da ta shirya cikin kayan baccin ta dogon wando da riga fare tas sannan ta tada sallah. Ta jima tana addu’a kan Allah ya kawo mata dauki sannan ta Mikewa jiki a sanyaye ta bude firij. Lemo ta dauko ta koma kan gado ta zauna. Wayar ta ta dauka ta latsa number Yaa Buhari. Da sauri ya dauka. Murya ta shagwabe ta ce, “Yaya shine ka manta dani ko?” Murmushi yayi ya ce, “Tayaya zan manta dake Sis. Na ta neman number ki ke da wife ban same ku ba.” Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, “To Yaya Ya hanya yasu Momy da Dady.” “Suna lafiya. Ince kuma kuna lafiya.” Ka…