RANAR NADAMA CHAPTER A
RANAR NADAMA CHAPTER A Sautin kida ne ke tashi cikin motar mai Dan karan dadi da nishadar da mai jin sa kallo daya za kayi mata ka tabbatar nishadine ya fado rayuwarta daga yanayin da take murmushi da rausayar da kai lokaci-lokaci ta na kai duban ta ga titi domin kaucewa afkuwar hadari. Wayarta da ke yashe cikin lokar motar ta shi ga burari da sauri ta kai duban ta kan fuskar wayar ganin sunan da yafito ya san ya ta murmusawa da sauri ta ta kai hannun ta ta dauka gami da latsa maballin amsa kira ta kara a kunne “amarya kin sha kamshi amarya bakya laifi ko kin kashe Dan mai gida” a ka fadi daga dayan Barin cikin yanayi na dariya ita ma rukayya dariya ta saki gami da cewa”ke kam kin shiga uku bunayya ke yanzu sai ki yarda ni amarya ce ai na wuce amaryar duk Wanda ki ka ji an tambata da sunan amarya to bincika zai iyayuwa ranar daurin aure ko kuma bayan an daura aure ana kokarin kai ta gidan mijin ta” shewa bunayya tayi gami da sakin guda har tafa hannu ka na iya jiyo sautin daga cikin wa…