MIJIN BUZUWA CHAPTER B KARSHE
MIJIN BUZUWA CHAPTER B KARSHE Yau take son ta gwada abubuwan da aikin boka dan Ondo wanda ya ja mata kunne da gujewa aikata kuskure tace zata tsare in sha Allahu. Ya shigo bai jima da dawowa ba ya fada wanka Nafisa ta shigo dakon kai tsaye tasamu yana ban dakin gurin wanka nan ta zauna a bakin gadon cike da jiran mijin nata. Ya fito daga ban dakin ta taso ta karbi duk wani abinda yake ma jikin shi tana mai gama daga goge jiki da shafan mai da saka turare da sauran su. Shidai ido kawai ya saka ma ta yaga iya gudunta don zuwa yanzu ya fara gano shirin ta sam bai yarda da wanan abinda take mashi ba . Ya gane sai tana son abu take mashi ladabin shegu a lokacin yake miji da zaran ta samu abinda take so shike nan ta koma ma halinta na I don’t care da ta saba dashi. Zama yayi a bakin gado yana jiran yaji ta inda zata bullo mashi ta dan yi dariya tare da karasowa wurin shi ta zauna itama. Sai bayan ta zauna ne tace samad a ranshi yace nasan da wanan kan tace wai yaushe ne zamu tafi sh…