YAR ALMAJIRA CHAPTER D KARSHE

YAR ALMAJIRA CHAPTER D KARSHE
YAR ALMAJIRA CHAPTER D KARSHE Tunda suka shiga mota Noor take kuka har suka isa gidan bata dena ba sunyi rarrashin har sun gaji kafin suka kaita d’akin Inna Kubra matar kawu dan bata amanar d’iyarsu sosai aka musu kar6a mai kyau kafin suka kaita d’akinta, basu dad’e a gidan ba suka juya zuwa gida aka barta tare da k’awarta d’aya da kuma y’ar mak’otansu duk da cewa zata girmi Noor din sosai amma kuma suna shiri na ban mamaki.  + Bayan shigowan Tasi’u ya nufi d’akin kawu dan amsa kiran da yake mishi, bayan sun gaisa kawu yace “dama ba wani abu bane face d’an k’aramin nasiha gareka d’ana, kasani cewa akwai wasu siffofin nagari dake tattare da kowani namiji wanda kowace macce ke so, Mijin dake son matar sa bayan aurensu fiyeda yadda yake sonta a layi, Miji mai kishin matarsa domin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace “duk wanda baya kishin matarsa bazai shiga Aljannah ba” sai kuma Mijin da ya dauki aure a matsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jindadin rayuwa kawai ba, wanda ya …