YAR ALMAJIRA CHAPTER C
YAR ALMAJIRA CHAPTER C Kwanaki sun shud’e watanni sun tafi kullun suna waya da Dr Affan da kuma Hajiya kuma kusan ko wani sati tana zuwa gidan domin duba su karshen zuwan da tayi kaya ta kawo musu kowa seti biyu atamfa da leshi dan suyi amfani dashi a salla tabbas basuda wani abun cewa a wannan mata se dai adduar fatan alkairi da ita da zuri’arta gaba d’aya domin kusan abunda mahaifiyar su zata musu kenan idan tana raye tabbas sun godewa ubangiji da wannan rahamar da yayi agaresu. Wahala dai babu irin wanda Innarsu bata sanya su kullun burinta ita da y’arta shine suga cewar sun tagayyara ayyuka dai ba sauki se abunda yayi gaba sedai sun yarda cewa wahala bata kisa domin ba yanzu suka fara sha ba kuma sun yarda cewa komai yanada lokaci da yardan Allah wata rana se labari. 2 Kamar kullun yauma bayan sun gama aiki suka d’iba abun bude bakinsu suka wuce dashi 6angarensu bayan ansha ruwa sukayi hira sosai kafin suka tafi sallar asham a masallacin unguwarsu suna dawo wa motar mahaifinsu na shi…