YAR ALMAJIRA CHAPTER B

YAR ALMAJIRA CHAPTER B
YAR ALMAJIRA CHAPTER B Washe gari da safe ta kira wayar sa taji akashe, haka tayi ta kira har yamma amma baya zuwa duk dai zance da yace wai swtchoff, karshe dai bayan sallar magriba ta kira Hajja Ghaji akan tazo ta raka ta gurin saurayin yayarta ko zata samu information akan inda zata sameshi. + 6angaren Dr Affan kuwa hankali kwance har yama manta da cewa wata ta kirashi jiya harta 6ata mishi rai don kuwa tunda ya tashi ya cire sim din data kira dashi yasa wani a cikin wayar yaji damuwarsa ta tafi. Meanwhile a 6angaren su Hajja Hadiza har sun tari dan adaidaita don shigowa anguwarsu Sule,sun koyi dace domin suna sauka suka hango shi a bakin masallaci, ba tare da tunanin komi ba suka karasa inda yake cike da jindadin ganinsa, shi kuwa mamaki ne ya kamashi akan meya kawo su a wannan lokaci kusan ishai, ganin cewa gunsa suka nufo yasa ya tashi yaje ya same su. “Hadiza lafiya na ganki a wannan lokacin kusan goshin ishai?” ya tambaya yana nazarinta “Lafiya ba lafiya ba yaya, dama munzo ne akan…