YAR ALMAJIRA CHAPTER A
YAR ALMAJIRA CHAPTER A Umma! umma!! umma!!! “kitashi karki mutu kibarmu a cikin wannan rayuwa me cike da tarin bakinciki da kuncin zuciya dan Allah umma kiyi hakuri ki bude idanunki” kuka sosai takeyi me cin zuciya, tana jijjiga ummanta dake kwanta akan wani tsamurarren katifa, ganin dai har yanzu umman taki motsawa yasa ta fita waje dan neman agaji, abun mamaki tana fitowa naga wani hadadden gida agefe me cike da abubuwan ban mamaki da al-ajabi, sake kallon ta nayi sannan na kalli d’akin data fito aciki, tunani nafarayi kodai 6angaren yan aiki ne ko kuma d’akin matar me gadi ne toh koma dai miye bari zan binciko mana daga baya.+ Wani me adaidaita ta tsayar sannan ta rokeshi akan ya taimaka mata su d’auko mahaifiyarta daga ciki, dafarko yak’i yarda saboda tsoron irin hali na d’an adam awannan zamanin daga baya kuma ya amince suka shiga suka fito da ita, basu tsaya ko inaba se government hospital dake cikin garin bama, kasancewar weekend ne asibitin shuru ba hayaniya ba kuma mutane…