SILAR AJALI CHAPTER C KARSHE
SILAR AJALI CHAPTER C KARSHE Tulin tsarabar da suka kaima Goggo ne ya rufe bakin ta fatanta a ce wani saurayin ne ya ma salma wannan kyautar ba ruwanta da ko da ace wani abin ne ya faru. Haka rayuwa tayi ta tafiya babu daɗi sai godiyar Allah, wulakanci yau daban na gobe daban, burin ta dai a samu Salmah da wani mugun hali ta samu abin yayatawa. Ana haka rannan salma ta wanke kayanta, taje daukan dutse guga da yake goggo ta daukeshi daga dakin Salmah takai nata, nan kuwa tayi fir ta tace “ba zan ba da ba, wa’inda suka haifo ku basu san zaku yi guga bane, Shegiya da ido kamar na mayu” Bata ce da ita komi ba ta saka hijabbinta na zuwa makaranta a yamutse ta tafi islamiyya, hakan ya kara kona ma Goggo rai don har ta dawo mita take akan zancen. Washegari ta same ta bayan ta kammala duk wani aiki da ke gaban ta ta ce mata ” dan Allah inje gida Batulu mai nika in goge, kin ga goggo hijabbin ya kara yamutsewa da na wanke” Ta karasa tana marairaicewa abinka da dan makaranta ga shi tana ganin ta k…