SILAR AJALI CHAPTER B

SILAR AJALI CHAPTER B
SILAR AJALI CHAPTER B ALKAWARIN ALLAH Sati biyu kawai aka kara kafin a ɗaura auren Imran da Rahanatu.  Ba’a yi wani shagali ba amma cikin sati biyun nan baba (mahaifiyar Haroon) ta kintsa ta da duk wani abin da ta san na gyaran jiki ne.  Fatar ta ya sha lalle don sati tayi tana Wanka cikin ruwan lalle.  Mata ke ta shiga da fice wanda mafi yawansu yan uwa da makota ne da Baba ta gayyata.  Bayan sallar isha’i aka ɗauke ta zuwa ɗakin da aka ware ma Imran a cikin gidan.  Tana kuka inna mairo kanwar baba ta riko ta. Faɗi take “shiga da kafar dama kina mai ambatar bismillah”  haka suka shiga ɗakin da ya sha daɓe da fentin farar kasa. Anyi kwanan amarci, amare da kawayenta, wa’inda duk kawayensu laminde ne. Washe gari daga cikin gida aka kawo masu abin kari, da kuma na rana,  bayan nan ne aka yi buɗan kai.  Da dare abokan ango suka shigo aka siya baki kafin a watse a barsu. Nan ne fa maganar kurame ya tashi don daga ita har shi ba wanda ke jin yaren wani. Da safe baba ta tada su,  nan ta fito da…