SILAR AJALI CHAPTER A

SILAR AJALI CHAPTER A
SILAR AJALI CHAPTER A Kwance ta ke kan gadon karfen ta, zuciyarta na bugu fiye da bugun sa, cikinta na murɗa mata tamkar mai shirin gudawa, duk da haka kwakkwaran juyi ma kasa yin shi ta yi, tsoro ne fal a cikin ranta Kasancewar ba ta san abinda daren yau zai zo mata da shi ba . Da ya ke wata ya kai ashirin da shida, duhun daren ya wuce misali, gari yayi baki kirin ko ganin tafin hannunta bata yi. Sassanyar iskar bazara da ke kaɗawa,da kuma kugin iska da ke tashi daga rassa da bishiyoyin kankarar bai hana zufa keto mata ta koina daga jikin ta ba, sai ma tsoron da ya ke daɗa shiga cikin ran ta don har ganin kamar gilmawar inuwar mutum take hakan ya sa ta kara gimtse idanunta gam, don bata ma son tsautsayi ya sa ta buɗe su. Duk da dai ba ta san takamamman lokaci a yanzu ba, ta san dai akalla karfe ɗaya na dare zai yi. “Ba shakka ya kusa zuwa, yanzun kuwa zai zo” Ta faɗa a ranta don kuwa kusan sati daya kenan a jere ya kan zo mata Idan ta na bacci sai dai kawai ta ji hannaye na bin kafar ta…