RAYUWAR ASMU CHAPTER 10
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 10 Kuka ta kuma fashewa da shi ta ce, “Meyasa? meyasa? Meyasa yaa Aslam? Me nayi maka da na cancanci haka.”+ Ta kuma fashe wa da kuka dan har numfashi ta na sarkewa. Mami ce ta fito ta tadda ta a hankalin da take ciki. Da sauri ta karassa gun ta. Ina har numfashin ta ya dauke Da sauri Mami ta kira suka tafi da Asma’u asibiti. Aslam kuwa ana can yau daurin aure. Duk da yau take ranar farin ciki a gunsa amman sai akasin haka. Dan damuwa sosai ya shiga na tinawa da tini da Asma’u ake daura auren nasu. Duk yadda yaso yai farin ciki ya kasa. Abokan sa kuwa dayawa duk basu je daurin auren ba dan ya riga ya koya musu son Amsa’u. Dukkan su mamaki suke sosai. Wasu kuma haushin Pretty suke ji. Wasu daga cikin abokan sa su suka hallaci daurin auren. Bayan an gama reception ya koma gida ne ya kwanta a daki. Ba abinda yake gani sai Asma’u da ke masa murmushi. Ido ya lumshe, ya rasa me yake damun sa. Gani yake kamar a mafarki wai ya auri Pretty. Mamaki yake sosai amman kuma sai wani abu ya …