RAYUWAR ASMAU CHAPTER 9

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 9
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 9 Kwanan Pretty biyu sannan ta koma gun malamin ta. Tana zuwa ya hau mata albishir da aikin ta yayi kamar me. Murna ta farayi. Malamin ya ce, “Sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba. Shine ki kula sosai sannan kafin aure kiyi kokari ki dawo dan akwai wani abu da za a karayi miki.” Godiya tayi masa, ya ce, “Kar ki damu da kin je gida zaki tadda abin mamaki.” Kudi masu yawa ta zube masa ta tashi tana masa godiya shi kuwa a ransa tinda ya kusan ce ta yaji a duniya ba wacce yake so kamar ta. Yayi Alkawari da duk daren dadewa sai ya mallake ta ta zama tasa gaba daya. Ya bata dama ne ta je wajen Aslam din amman yayi alkwarin shi da kansa zai raba su dan ya same ta. Ita kuwa Pretty gida tayi tana ta murna. ********************************************** Aslam ne zaune a dakin sa yana waya da Asma’u. Duk wayar da suke kara kwantar mata da hankali yake, sosai take samun nutsuwa in tana tare da Aslam. Sai dai kwanan nan tana yawa mafarkai akan Aslam, wanda in ta zauna ita kadai tai ta ku…